Faransa ta gama farmaki kan 'yan ta'adda

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan sanda sun kama mutane biyu a Paris.

Hukumomin Faransa sun ce an kawo karshen gagarumin farmakin yaki da ta'addanci a arewacin Paris.

Sai dai har yanzu akwai 'yan sanda da sojoji masu tarin yawa da aka baza a yankin Saint Denis.

An kashe mutane biyu da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai birnin Paris a wani gida, ciki har da wata mace wadda ta tarwatsa kan ta.

IS ta fitar da bidiyo kan harin Paris

A gefe guda kuma, 'yan kungiyar IS sun fitar da wani bidiyo wanda ke nuna su suna murnar nasarar da suka yi a hare-haren na birnin Paris.

Bidiyon ya nuna wasu 'yan kungiyar guda uku, wadanda suka ce su suka kai hare-haren Paris domin yin ramuwar-gayya kan wahalar da 'yan uwansu Musulmai suke sha a hannun Faransa.

Sun yaba kan hare-haren da suka kai a baya, suna masu yin alwashin kai karin hare-hare.