Algeria ta maido da 'yan Niger 251 gida

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Hukumomin Algeria sun maido da 'yan Niger 251 mafiyawancinsu mata zuwa gida.

Wata jami'ar gwamnati a jihar Damagaram ta ce cikin wadanda aka tuso keyar ta su, 220 sun fito ne daga garin Kantche, sai 19 daga Magarya.

Yayinda bakwai daga cikinsu kuma suka fito daga Tanut, sai kuma biyar daga Taketa.

Wasu daga cikin matan sun shaida wa BBC cewa a wasu lokutan sukan sayar da kadarorinsu domin yin wannan tafiya mai cike da hatsari ta cikin hamada.

Gwamnatin Niger dai na tallafawa matan da jari domin su rinka yin sana'oi amma hakan bai sa sun daina wannan tafiya ba.