BH: Chadi ta tsawaita dokar ta baci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya ma Chadi ta yanke wa wasu mayakan Boko HAram hukuncin kisa.

A ranar Alhamis ne majalisar dokokin Chadi ta yanke shawarar tsawaita dokar ta baci a yankin Sahel, a kokarinta da kare hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram da ke Najeriya.

A ranar Laraba da daddare ne gaba daya 'yan majalisar 147 suka amince da dokar, har sai zuwa watan Maris na shekarar 2016.

Tun a ranar tara ga watan Nuwamba ne gwamnatin Chadi ta sanya dokar ta baci a yankin, bayan wani harin kunar bakin wake da wasu mata suka kai, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da jikkata mutane 14 a Ngouboua.

Kazalika, majalisar dokokin ta bai wa gwamnan lardin ikon haramta zirga-zirgar mutane a yankunan da yake so a wasu sa'o'i.

Zai kuma iya bayar da umarnin yin bincike gida-gida da rana da kuma dare, a karkashin umarnin mai shigar da kara na jamhuriyyar da kuma kwato makamai.

Mayakan Boko Haram na kai hare-harensu a kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi, wadanda suka yi sanadiyyar rayuka da dama.