Ana bincike kan mutuwar sojin Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin sun mayar da martani.

Rundunar sojin Nigeria ta ce tana ci gaba da tattara bayanai game da rahotannin dake cewa an kashe sojojin kasar kimanin 35 sakamakon harin 'yan Boko Haram a garin Gudunbale da ke jihar Borno.

Kwamandan rundunar Operatin Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram a arewa maso gabas, Manjo Janar Yusha'u Mahmud Abubakar, ya shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram sun kai hari a kan dakarunsu, amma sun fatattaki maharan.

Manjo Janar Abubakar ya ce suna gudanar da bincike kafin tantance gaskiyar abin da ya faru.

Ya ce duk da suna gudanar da bincike, amma babu kanshin gaskiya game da kisan da kuma bacewar dakarunsu sama da dari.

Kimanin kwanaki biyar da suka wuce dakarun Najeriya suka kama garin na Gudunbale.