Faransa za ta tsaiwaita dokar ta baci

Majalisar dokokin Faransa Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Majalisar dokokin Faransa

Majalisar dokokin faransa tana gab da amince wa da kara tsawon wa'adin gagarimin matakin ta baci da aka ayyana a kasar daga kwanaki shida zuwa watanni uku.

'yan majalisar wakilan kasar kuma za su tattauna yadda girman dokar zai kasance.

Ana dai son sauya dokokin kasar da suka jibanci mutanen da za yi wa daurin talala a gidajensu da kuma ba wa 'yan sanda damar shiga gidan mutane su yi bincike ba tare da takardar sammace daga kotu ba.

A baya dai an ayyana kwanaki shida domin daukar gagarimin mataki a kasar tun bayan hare haren ranar Juma'aa Paris.