Paris: Mahara sun yi amfani da gudun hijira

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An yi kaca-kaca da gawar Abdelhamid Abaaoud.

Firayiministan Faransa ya ce wasu daga cikin mutanen da ake alakantawa da hare-haren da aka kai a kasar cikin makon jiya, sun yi amfani ne da matsalar 'yan gudun hijira suka shiga Turai ba a sani ba.

Mista Manuel Valls ya yi gargadin cewa tsarin tafiye tafiye a kasashen Turai ba tare da amfani da Paspo ba, ya na fuskantar barazana, muddin dai ba a kara inganta matakai a kan iyakokin kasashen nahiyar ba.

Gwamnatin Faransa ta ce sai bayan da aka kaddamar da hare-haren a kasar ne, sannan ta samu labarin cewa mutumin da ake zargi da zaman jagoran maharan, Abdelhamid Abaaoud, ya bi ta Girka bayan ya dawo daga Syria kafin ya shiga kasar.

Ba a tabbatar da ko Abdelhamid ya bayyana kansa a matsayin dan gudun hijira ne koko a a ba.

A jiya Alhamis ne aka tabbatar da mutuwar shi lokacin da 'yan sanda suka kai samame arewacin Paris inda suke farautarsa.

Faransa ta gabatar da wani daftarin kuduri ga kwamitin tsaro na MDD, inda ta ke neman goyon bayan kasashen duniya don yakar kungiyar IS.