Zai yi wuya a shawo kan gibi tsakanin maza da mata

Hakkin mallakar hoto AP

Wani rahoto da kungiyar masana tattalin arziki ta duniya, World Economic Forum, ta fitar ya ce zai dauki tsawon lokaci kafin a cimma daidaito a tazarar karbar albashi tsakanin maza da mata.

Rahoton ya ce a yanzu haka mata na karbar yawan albashin da ake biyan maza a shekarar 2006.

Kungiyar ta ce a shekarun baya bayan nan an samu tsaiko a kokarin da ake yi domin shawo kan wannan gibi duk da cewa ana samun karuwa a yawan matan da ke samun aiki.

Kungiyar ta kara da cewa a yanzu haka mata kusan miliyan 250 ne ke cikin ma'aikatan duniya idan aka kwatanta da shekaru goma da suka gabata.

Haka kuma rahoton ya ce an samu karuwa a yawan mutanen da ke karatu a jami'oi a kasashe da dama sai dai duk da haka mata kalilan ne suke samun mukamai na kwararrun ma'aikata.

Rahoton dai ya yi nazari a kan damar da 'yancin da maza da mata suke da shi a kowace kasa a fannin kiwon lafiya da ilimi da tattalin arziki da kuma siyasa.