An katse intanet a Bangladesh bisa kure

Hukumomi a Bangladesh sun ce katsewar hanyoyin intanet da aka samu a kasar, wanda ya dauki fiye da sa'a guda wani kuskure.

Jami'ai a kasar sun sanar da cewa an rufe shafukan sada zumunta na Facebook da Viber da WhatsApp bayan wani hukuncin kotun koli da ya tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa wasu maza biyu da aka samu da aikata laifukan yaki.

Sai dai hukumar da ke kula da hanyoyin sadarwa ta kasar ta ce kuskure ta yi data katse hanyoyin intanet a fadin kasar.

Wata jaridar kasar ta ce daga karfe daya na rana a kasar ne intanet din ta dauke ranar Laraba, kuma intanet din bai dawo ba har tsawon minti 75.

Shugaban hukumar kula da hanyoyin sadarwa a kasar, Mista Shahjahan Mahmood ya ce an katse hanyoyin sadarwa na shafuka sada zumuntan ne kamar yadda aka tsara daga farko domin tabbatar da tsaro.

Amma ya ce babu wani umurni da aka bayar na yanke hanyoyin intanet, sai dai an samu matsala ne a wajen rufe hanyoyin sadarwa na shafukan sada zumuntan.

Masu sana'o'i a kasar sun yi korafin cewa sun kasa kulla cinikayya a lokacin da intanet din ta dauke, inda har shugaban wani kamfani ya shaidawa jaridar The Daily Star cewa illar da daukewar intanet ta janyo wa sana'o'insu za ta dade.