Swaziland na dab da kawar da maleriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana san ran kawar da maleriya a Swanziland kafin karshen shekarar 2017.

Wani masanin kiwon lafiya a Jami'ar California ya ce kasar Swaziland na dab da kawar da cutar zazzabin cizon sauro.

Richard Feachem, wanda ke cikin masu rajin ganin an kawo karshen cutar, ya ce Swaziland za ta kawar da ita a karshen shekarar 2016 ko farkon shekarar 2017.

A cewar sa, adadin mutanen da ke kamuwa da cutar ya ragu da kashi 99 cikin 100 daga shekarar 2000 zuwa 2014.

Mr Feachem ya ce kasar ta dauki matakan kawar da cutar, cikinsu har da yin amfani da magungunan cutar da yin amfani da gidan sauro a lokacin kwanciya.

Hukumomi a kasar sun ce mutane 230 kawai suka kamu da cutar maleriya a shekarar 2013.