Saudiyya ce take tallafa wa IS — Assad

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Syria, Bashir El Assad

Shugaban Syria Bashir Al-Assad ya yi zargin cewa kasashe uku ne suke taimaka wa kungiyar IS, cikinsu har da Saudiyya.

Assad, wanda ya musanta zargin da ake yi masa cewa Syria cew ke mara wa 'yan ta'addan baya, ya kara da cewa sauran kasashen da ke goyon bayan IS su ne Turkiyya da Qatar.

Assad ya yi wannan zargi ne a hirarsa da wani gidan talabijin na kasar Italiya.

Ya kara da cewa ba za a yi zabe a kasarsa yanzu ba tunda wani bangare na kasar yana hannun mayakan IS.