Yau ce ranar Makewayi ta Duniya

An sanya ranar 19 ga watan Octoban kowacce shekara ta zamo ranar Makewayi ta Duniya.

Ma'anar ranar dai ita ce jawo hankalin duniya ga mutanen da ba su da tsaftataccen muhallin da ya dace da kuma makewayi.

Kididdiga ta nuna cewa sama da mutane biliyan biyu, a fadin duniya ba su da tsaftataccen muhallin da ya dace sannan kusan mutane biliyan daya suna ba-haya a waje ne.

A Najeriya, wasu alkaluma na nuni da cewa kashi 71 cikin 100 na al'ummar kasar ba sa samun damar amfani da makewayi, al'amarin da ke barazana ga lafiyarsu, da mutuncinsu.