An gano sojin Nigeria da suka bata

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rundunar sojin ta ce dakarunta sun koma wurin aikinsu.

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta da suka bata a lokacin da suke aiki a garuruwan Gudumbali da Kareto na jihar Borno sun koma rundunarsu da ke yankin.

A farkon makon nan ne dai rahotanni suka ce 'yan kungiyar Boko Haram sun yi wa sojin kwantan-bauna, a lokacin da suka kai musu hari a Gudumbali.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Kanar Sani Kukasheka Usman, ya aikewa manema labarai, ya ce "Sojin Najeriya da ke aiki a garuruwan Gudumbali da Kareto sun fuskanci koma-baya a makon nan. Sai dai yanzu al'amura sun koma daidai".

Kanar Kukasheka ya kara da cewa kafafen watsa labarai sun kambama rahotannin da suka bayar kan lamarin.

A cewar sa, "Dakarun sun koma wurin aikinsu domin jiran a ba su umarni kan abin da za su yi nan gaba".