Nigeria za ta saka $250m a asusun ko-ta-kwana

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Minsitan kudi na Najeriya, Kemi Adeosun.

Najeriya za ta saka dala miliyan 250 a cikin asusunta na ko-ta-kwana, wato Sovereign Wealth Fund, wanda shi ne karon farko da ake sanya kudin a asusun a duk tsawon wannan shekarar.

Kudaden da gwamnatin kasar ke ajiyewa domin gobe na karuwa duk da faduwar farashin danyen man fetur.

An jima wannan asusun na ko-ta-kwana bai samu kudi ba, tun a bara lokacin da gwamnatin da ta shude da saka dala biliyan daya a ciki.

Sai dai wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnonin jihohin kasar suka ce ba za su iya ci gaba da biyan Naira 18,000 a matsayin mafi kankantar albashi ba, saboda faduwar farashin danyen man da ya shafi karfin tattalin arzikin kasar.