Za a daina safarar mutane a Asiya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugabannin kasashen da ke kudu maso gabashin Asiya

Shugabannin kasashe goma da ke sassan kudu maso gabashin Asiya sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya da za ta magance matsalar safarar mutane a yankin.

An amince da wannan yarjejeniya ce a wajen wani taro na kungiyar kasashen Asiyan da ke yankin kudu maso gabashi wanda a ka yi a Kuala Lumpur.

Kuma taron ya tsara hanyoyin da za a bi wajen dakatar da wannan mummunar dabi'a tare da kare wadanda ake safarar.

Batun ya ja hankalin kafofin yada labarai ne a farkon shekarar nan a lokacin da dubban 'yan gudun hijira yawancin su 'yan kabilar Rohingya suka makale a jirgin ruwa, bayan da kasar Thailand ta katse hanyoyin da masu safarar mutane ke bi ko suke amfani da su.