Belgium ta daga matsayin ankararwa kan tsaro

Hakkin mallakar hoto

Firayiministan Belgium Charles Michel yace sun sami bayanai da ke nuna yiwuwar kai hari makamancin wanda ya auku a Paris a makon da ya wuce.

Masu gabatar da kara a Belgium sun ce an gano wasu makamai amma ba bama bamai ba a gidan wani mutum da aka kama wanda ake zargi da hannu a harin Paris.

An dakatar da zirga zirgar jiragen kasa a cikin birnin Brussels da kuma sauran jiragen kasa sannan an dage wasu wasannin kwallon kafa da aka shirya bugawa.

An gargadi mutane su guji wuraren taruwar jama'a.