'Yan bindiga sun kashe Basarake a Fotokol

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu da harin Boko Haram ya ritsa da su

Akalla mutane 10 ne suka mutu lokacin da wasu mata 4 suka kai tagwayen hare-haren kunar bakin wake a garin Nije kusa da Fotokol mai iyaka da Najeriya.

Harin na farko wanda wata budurwa ta kai ya hallaka akalla mutane 5 tare da basaraken gargajiya na garin Nije.

Wata 'yar kunar bakin wake ce ta shiga gidan basaraken, inda bayan ta yi sallama, mutanen gidan sun hadu wuri guda, sai ta tayar da bom din dake jikinta.

Wasu mutanen kimanin 10 sun jikkata a hare-haren.

Bayan wasu 'yan mintuna kuma sai sauran 'yan mata 3 suka kai hari na biyu wanda bai haddasa asarar rayukan jama'a ba.

Wasu majiyoyin tsaro sun ce shekarun 'yan matan 4 basu wuce sha biyar-biyar ba.

Gwamnan Lardin arewa mai nisa Midjinyawa Bakary ya ce an kai jami'an tsaro garin.

Al'uman garin Fotokol da kewaye sun fada a cikin mawuyatsin halin rayuwa tun lokacin da salon kai harin kunar bakin wake ya bullo.

Fiye da mutane 100 ne hare-hare 20 suka hallaka a cikin watanni 5 da farawar lamarin.