Israila ta rufe gidan radion Falasdinawa

Gidan radion Falasdina a Hebron Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Gidan radion Falasdina a Hebron

Jami'an tsaron Israila sun kai samame tare da rufe wani gidan radiyo na Falasdinawa a Hebron.

Karo na biyu kenan da mahukuntan Israilar suke daukar irin wannan mataki.

Sojojin Israila sun afka gidan radiyon Alkhali suka baiwa ma'aikatan takardar umarnin soji na rufe gidan radiyon na tsawon watanni shida.

Sojojin Israilar sun zargi gidan radiyon da yada batutuwan da ke karfafa ayyukan tarzoma da tunzura bore akan al'ummar Israila.

Gwamnatin Falasdinawa ta yi Allah wadai da matakin Israilan a matsayin keta dokokin kasa da kasa.