Mutane 40 sun mutu a ruftawar kasa a Myanmar

A kalla mutane 40 sun mutu wasu da dama kuma sun bata bayan ruftawar kasa a arewacin Myanmar.

Tarin shara ce ta rufta da mutanen a wani wurin zubar da shara da kamfanin Jade ke amfani da shi a jihar Kachin.

Yawancin wadanda suka rasu ana zaton mutane ne wadanda suke neman tarkace a bola wadanda kuma ke zama a kusa da wurin.

Suna laluben sharar ce da hannu domin samun karafa da za su sayar domin samun kudi.