Raqqa: Fararen hula na cikin mawuyacin hali

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan IS ne ke da karfi a birnin Raqqa

Wani mazaunin birnin Raqqa na Syria inda mayakan IS ke da karfi ya fadawa BBC cewa halinda fararen hula ke ciki a can ya tabarbare.

Mutumin-- wanda dan wata kungiya ne dake kin jinin fafutukar da mayakan IS ke yi, wanda kuma baya son a bayyana sunansa-- ya ce karuwar farmakin da ake kaiwa ta sama tun lokacin da aka kai hare- haren Paris ya janyo kashe karin fararen hula ko kuma jikkata su.

Ya kuma ce babu wutar lantarki a kusan gabakidaya garin sannan an hana mutane amfani da Intanet

Da wuya fararen hular su bar Raqqa, saboda mambobin kungiyar IS ne kadai ke a wuraren binciken duba hawa dake fadin garin