An zartar da kisa kan 'yan adawa a Bangladesh

Image caption Firayiministan Bangladesh Sheikh Hasina

An tsaurara matakan tsaro a Bangladesh bayan da aka zartar da hukuncin kisa a kan wasu jagororin 'yan adawa biyu da aka samu da aikata laifukan yaki lokacin da kasar ta yi yakin neman 'yan cin kai da Pakistan a 1971.

An zartar da hukuncin kisa kan Salahuddin Quader Chowdhury da Ali Ahsan Mohammad Mujahid ne a gidan kurkuku na babban birnin kasar Dhaka.

Salahuddin wani dan siyasa ne mai fada aji wanda ya yi ta samun nasara a zaben dan majalisa a kasar har sau 6, yayin da Ali Ahsan Mujahid kuwa, jagora ne a jam'iyyar Musulunci mafi girma a kasar, Jamaat el-Islami.

Hukuncin da aka yanke wa mutanen a farko ya janyo tashe-tashen hankali a fadin kasar, inda ake fargabar zartar da hukuncin yanzu, zai iya haddasa wata fitinar sabuwa.

Firayiministan kasar Sheikh Hasina ta musanta zargin da ake yi cewa an kashe jagororin adawan ne saboda dalilai na siyasa.