China ta zargi Amirka da tsokana kan tsibirai

Hakkin mallakar hoto US Navy

China ta kare matsayinta kan gine ginen da ta yi a yankunan tsibiran da ake takaddama a kan su a kudancin kogin Chinan, tana mai cewa ba ta da niyyar tura sojoji a yankin.

Da yake jawabi a taron kolin kungiyar raya cigaban kasashen gabashin Asia a Kuala Lumpur, mataimakin ministan harkokin wajen China Liu Zhenmin ya zargi Amirka da tsoka da kuma neman tada husuma saboda tura jiragen yaki na ruwa zuwa yankin a watan da ya gabata.

China dai ta yi ikrarin cewa galibin kogin yana cikin yankin kasarta ne, sai dai kuma wasu kasashen hudu na gabashin Asia su ma sun yi ikrarin mallakinsu ne.

Amirka ta tura jiragen yaki na ruwa da jiragen sama zuwa yankin a makonnin da suka wuce inda tace ta na so ne ta tabbatar da yancin tafiye tafiye ta ruwa ba tare da tsangwama ba.