Mutane da dama sun mutu a Myanmar

Hakkin mallakar hoto Getty

Mutane da dama ne dai suka mutu sakamakon ruftawar kasa a wani wurin hakar ma'adanai a arewacin Myamnar

Kawo yanzu masu aikin ceto sun sami gano gawarwakin mutane 90 daga cikin wadanda kasar ta rufta da su.

Akwai dai mutane da dama wadanda har yannzu ba a gano su ba sai dai ma'aiktan ceto na cigaba da lalube.

Wakilin BBC a Myanmar yace ana tsammanin yawan wadanda suka rasu zai iya karuwa sakamakon girman ruftar kasar.

Wannan shine hadari mafi muni da aka fuskanta da ya shafi hakar ma'adanai a kasar.

Kasar ta rufta da mutanen ne lokacin da tarin sharar ma'adanai da ake jibgewa a wurin zubar da shara a jihar Kachin ta fada a jiya Asabar.