Faransa za ta zafafa kai hare-hare kan IS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Francois Hollande zai gana da Obama a wannan makon.

Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya ce kasarsa za ta zafafa hare-haren da take kai wa kan mayakan kungiyar IS a Syria da Iraki.

Hollande ya yi wannan bayani ne a Paris bayan ya gana da Firai Ministan Biritaniya David Cameron.

Mista Hollande ya tabbatar cewa za a fara amfani da babban jirgin ruwa mai daukar jiragen sama na Faransa, Charles de Gaulle, wajen kai hare-haren kan kungiyar ta IS.

A nasa bangaren, Mista Cameron ya ce sun amince su kara zage-dantse kan hadin kan da suke yi wajen yaki da 'yan ta'dda, ciki har da yadda za su kara taimakawa juna da bayanan sirri da na jiragen sama.

A wannan makon ne Mista Hollande zai gana da shugabannin kasashen Amurka da Rasha kan yaki da ta'addanci.