Taron kasashe masu albarkatun iskar gas

Hakkin mallakar hoto Getty

A ranar Litinin ne shugaban Nigeria Muhammadu Buhari da takwarorinsa na kasashe masu albarkatun iskar gas ke fara wani taro karo na uku a Iran.

Taron -- wanda shi ne karo na uku -- zai yi nazari ne kan yadda kasuwar iskar gas ke gudana a duniya da kuma hanyoyin bunkasa iskar gas da kasashen ke samarwa.

Najeriya dai na da dimbin iskar gas sai dai har yanzu kona shi ake yi sabanin yadda wasu kasashe irin su Iran ke amfana da nasu.

Rashin amfani da arzikin iskar gas din da Nigeria ke da shi ne yasa ake sare dazuka a kasar domin yin girki, abinda ke yin barazana ga muhalli.