Mahama zai sake takarar shugabancin Ghana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Mahama yana shan suka saboda tabarbarewar tattalin arzikin Ghana.

Jam'iyyar National Democratic Congress (NDC) da ke mulkin Ghana ta amince da gagarumin rinjaye Shugaban kasar John Mahama ya sake yin takara a zaben 2016.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce kusan kashi 95 cikin dari na 'yan jam'iyyar da suka kada kuri'a a zaben fitar da gwanin da aka yi ranar Asabar da Lahadi ne suka amince Shugaba Mahama ya yi takara a karo na biyu.

Mista Mahama ya godewa 'yan jam'iyyar, sannan ya bayyana irin ayyukan da ya yi domin bunkasa harkar wutar lantarki da tattalin arziki, duk da rahotannin da ke cewa tattalin arzikin kasar yana tafiyar hawainiya kuma darajar kudin kasar, cedi, tana raguwa.

Mahama ya ce, "A matsayina na shugaba na san cewa ba kowa ne ya gamsu da abubuwan da na yi a shekaru uku ba. Ama duk da haka na ji dadin amincewar da na samu daga NDC, kuma na sha alwashin jagorantar jam'iyyar domin mu samu nasara a zaben shekarar 2016."