'Yan wasan guje-guje sun yi zanga-zanga a Kenya

Image caption 'Yan wasan Guje-guje

Wasu 'yan wasan guje-guje da tsalle tsalle sun mamaye Shelikwatar hukumar kula da wasanni ta kasar Kenya inda suka hana jami'ai shiga.

Wakiliyar BBC , Anne Soy ta ce suna so jami'an kula da guje-guje da tsalle-tsalle na Kenya, AK, su sauka akan zargin cin hanci da ke da alaka da wata yarjejeniya da kamfanin Nike.

Sai dai mataimakin shugaban AK, David Okeyo ya musanta zargin.

'Yan wasan guje-guje da tsalle-tsallen sun kuma dorawa ma'aikatan laifi a kan kasa magance cin hanci a wasanni.

Dick Pound - wanda ke bincike akan cin hanci a hukumar wasan guje-guje na duniya, IAAF - ya ce 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Kenya suna da "matsala sosai" da shan kwayoyin kara kuzari.