An fara makokin kwanaki uku a Mali

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojin kasashen waje sun taimaka domin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

An fara zaman makokin kwanaki uku a kasar Mali bayan harin da 'yan bindiga suka kai a wani Otal da ke Bamako, babban birnin kasar ranar Juma'a.

Haren-haren da aka kai a Otal din Radisson Blu sun yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 19.

Dakarun kasar Mali da takwarorinsu na wasu kasashen duniya sun kutsa kai cikin otal din inda suka kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

An kashe 'yan bindiga biyu.

Kungiyoyi biyu na masu tsattsauran ra'ayin addini sun dauki alhakin kai hare-haren.

Sai dai har yanzu ba a san kasashen da 'yan bindigar suka fito ba.

Amma wata majiya ta shaida wa BBC cewa 'yan bindigar na yin turanci lokacin da suka kai harin.