Ungozomar da ke hana kaciyar mata

Image caption Aissa Edon ita ce ungozomar da ke kokarin hana kaciyar mata

Aissa Edon na da shekaru shida lokacin da yadikkonta ta dauke ta tare da kanwarta 'yar shekara daya ta kai su a ka yi musu wani abu na bankwana da kasar Mali.

Wannan abu kuwa shi ne kaciyar mata.

A kalla haka Aissa ke tunanin yadikkonta na kallon al'amarin.

A yanzu Aissa na aiki a London a matsayin Ungozoma, ta kware a taimakon mata matan da aka taba yi musu kaciya.

Ta zanta da wakiliyar BBC Smitha Mundasad, a wani shirin rediyo cikin shirye-shiryen mata 100 na BBC.

"Radadi da ihu"

Aissa mace ce kyakkyawa mai kirki da saukin kai, wacce ta gayyace ni zuwa gidanta a kudancin birnin London.

Ta shaida min a nutse cewa tana son kawo karshen kaciyar mata ko da hakan na nufin rasa rayuwarta ne.

Ta ce, "Abin takaici har yanzu ina tuna komai na yadda aka yi min kaciya. Ina iya tuna wajen.

Ta kara da cewa, "Ina iya tuna ihun da na dinga yi, da radadin da na ji. Ke kan ki idan kina jin ihun sai ki ga kamar wani ne ke yi amma daga baya sai ki gano cewa ai ke ce mai yin ihun."

Aissa bata yi bayani sosai a kan kuruciyarta ba, amma jim kadan bayan da aka yi mata kaciya, sai ta bar Mali ta koma Faransa sai wasu suka mayar da ita 'yar su.

A lokacin da ta fara rayuwa a sabuwar kasarta dole ta dinga kokarin magance matsalolin da take fuskanta sakamakon yanka ta da aka yi.

Ta kamu da cutar yawan yin fitsari da kuma yawan jin zafi kamar ana sukarta da wuka, haka ta yi ta fama kullum har ta kai shekara 23.

A lokacin da take cikin shekaru 20 ta samu wani likita Bafaranshe wanda ya yi mata tiyata.

Amma, idan har ta rabu da radadin da yake ji a jikinta, to fa ba ta rabu da hargitsin da kwakwalwarta ke ciki ba.

Ta yi ta kamfe na nuna adawa da kaciyar mata saboda tana jin cewa ya zama wajibi ta yi hakan ko don kanwarta da ta yi fatan dama ta iya cetonta.

Aissa ta ce , "Amma daga irin abin da nake yi yanzu, na san zan ceci wasu yaran."

Ba ta taba tattauna maganar da 'yar uwarta ba, amma a lokacin da take karantar aikin Ungozoma ta runtse idonta ta tattauna da mahaifinta a Mali.

Kuma a wannan lokaci ne aka rufe batun, a cewarta.

"Fito-na-fito"

Ta ce min bata je wajen domin kure shi ba, ko don ta gaya masa abin da ya faru ga ita ba dai-dai bane, sai dai domin ta tattauna da shi kan gaskiyar abin da ke cikin yi wa mata kaciya da illolin da hakan ke iya jawowa.

Wannan ne karo na farko da wani ya taba yi masa magana a kan hakan, duk da cewa ya zamo wani bangare na al'adarsu.

Ya saurara ya kuma yi kuka.

Kuma duk da cewa bata roki wani abu daga gare shi ba, ya yi alkawarin ba wacce za a sake yi wa kaciya cikin ahalinsa.

"Gardamar haihuwa"

A yanzu haka Aissa tana aiki domin wayar da kai da kuma hana yi wa mata kaciya a sauran wurare.

Babban aikinta shi ne taimakawa mata masu ciki a London wadanda aka taba yi musu kaciya a wani wajen.

Samun ciki shi ne lokaci ma fi hadari, inda a lokacin ne masu ciki ke gaya wa ungozomar da ke kula da su abin da ya same su, ko da kuwa ba su taba gayawa kowa ba tsawon shekaru.

Kuma yana da matukar muhimmanci Ungozomomin su sani.

A mafi yawancin lokuta, yanka da dinkin da ake yi wa matan na iya sa matancinsu ya kara kankancewa ta yadda ba za su iya haihuwa da kansu ba.

Kuma idan har ba a yi musu tiyata don cire dan da gaggawa ba, to jariran na iya fuskantar hadarin mutuwa.

A nan tana kokarin taimakon mata watanni da dama kafin su haihuwa, ko kuma idan za ta iya tun kafin ma su samu cikin.

Aissa ta ce, "ba wai domin abin da ya faru da ni kawai ba, don taimakonsu ne. Idan suka zo ganina to abinda ya danganci labarinsu ne ba nawa ba."