Ebola ta sake bulla a Liberia

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption A watan Satumba mutanen Laberiya suka yi farin ciki sakamakn ayyana kasar a matsayin ba bu sauran mai Ebola

Wani matashi da aka yi wa gwajin cutar Ebola aka kuma gano yana dauke da ita ya mutu a Laberiya.

Wannan ita ce mutuwa ta farko da aka yi sakamakon cutar tun bayan da aka ayyana cewa babu sauran cutar ta Ebola a Laberiya, a karo na biyu a watan Satumba.

Matashin mai shekara 15 ya mutu ne a wata cibiyar kula da lafiya da ke kusa da Monroviya babban birnin kasar.

A yanzu ana kula da mahaifinsa da dan'uwansa a cibiyar, wadanda su biyu ne kadai aka tabbatar sun kamu da cutar a halin yanzu a kasar.

Fiye da mutane 4,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar Ebola a Laberiya, tun farkon barkewarta a bara.