Boko Haram: An dage bikin nuna tufafi a Nijar

Image caption Ana yin bikin nunin tufafin a duk shekara.

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun dage bikin nuna tufafin gargajiya na Afrika, FIMA da ya kamata a soma ranar Laraba a Yamai, babban birnin kasar.

Shugabannin tsare-tsaren bikin sun ce sun dauki matakin ne saboda matsalolin rashin tsaro da kasar ke fuskanta.

Baje kolin tufafin Afirka na FIMA dai na daga cikin muhimman bukukuwan nuna al'adu da ake yi a Nijar.

Kungiyar Boko Haram ta matsa kai hare-hare a wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar, inda ta kashe mutane da dama tun daga farkon wannan shekarar.