Turkiyya ta harbo jirgin saman Rasha

Hakkin mallakar hoto
Image caption Turkiyya ta yi wa matukan jirgin gargadi.

Jiragen yakin Turkiyya sun harbo wani jirgin saman sojin Rasha a kan iyakar kasar Syria.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce wasu jiragen saman Turkiyya samfurin F-16 ne suka harba makamai masu linzamin da suka yi sanadiyar faduwar jirgin na Rasha samfurin Su-24 lokacin da yake wucewa ta sararin samaniyar Syria.

Sai dai jami'an rundunar sojin Turkiyya sun ce sai da aka yi wa matuka jirgin Rashan gargadin cewa yana keta sararin samaniyar Turkiyya amma ba su daina ba, lamarin da ya sa aka harbo shi.

Mista Putin ya bayyana harbo jirgin a matsayin wani "yankan-baya" da masu mara wa 'yan ta'adda baya suka yi.

Matukan jirgin biyu sun fice daga cikinsa kafin a harbo shi a lardin Latakia da ke cike da tsaunuka.

Wannan ne karon farko da jirgin Rasha ke faduwa a Syria tun bayan da kasar ta kaddamar da hare-hare ta sama a kasar domin ta taimaka wa Shugaba Bashar al-Assad a yakin da yake yi da 'yan tawaye.