An daina bikin ranar 'yanci a Tanzania

Hakkin mallakar hoto AFP

Sabon shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya soke bikin ranar 'yanci na kasar amma a maimakon hakan ya ba da umarnin a yi gangamin tsaftace muhalli.

A wani jawabi da Shugaba John ya yi a gidan talabijin na kasar, ya ce zai zamto abin kunya suka kashe makudan kudade a kan bikin ranar yanci a yayinda 'yan kasar ke mutuwa da cutar amai da gudawa.

Cutar amai da gudawa ya yi sanadiyar mutuwar kusan mutane 60 a Tanzania a watanni uku da suka wuce.