AIDS: MDD na shirin kara yawan tallafi

Hakkin mallakar hoto un
Image caption Majalisar Dinkin Duniya na son fadada ayyukanta na bayar da taimakon cutar AIDS

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tsarinta na rubanya yawan mutane masu dauke da cutar HIV ko AIDS da ke samun magani, cikin shekaru biyar.

Majalisar za ta yi haka ne a karkashin shirinta na yaki da cuta mai karya garkuwar jiki.

Shirin na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, duk da cewa yanzu haka mutane miliyan 15 ne ke samun maganin cutar ta AIDS, akwai kuma wasu masu fama da cutar miliyan 22 da basa samun magani kwata-kwata.

Yawancin wadanda basa samun maganin dai suna kasashe ne masu tasowa, kuma galibi ba su ma san suna dauke da cutar ba.

Majalisar Dinkin Duniya na son ta fadada ayyukanta wadanda aka gwada aka kuma samu nasara a kansu, da suka hada da wayar da kai da kuma yadda za a kare kai daga kamuwa da cutar ta HIV a tsakanin mata da yara, da kuma inganta hanyoyin gwajin cutar a yankunan karkara.