Boko Haram, IS, al-Qaeda na shirin kai hari — Amurka

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Amurka ta ce ba 'yan kasarta ne kawai ke fuskantar barazana ba.

Amurka ta ce kungiyoyin 'yan ta'adda na IS, al-Qaeda da Boko Haram na shirin kaddamar da sabbin hare-hare a yankuna daban-daban na duniya.

Amurka ta bayyana haka ne a wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar, inda ta gargadi 'yan kasarta da su yi kaffa-kaffa kan wuraren da za su kai ziyara.

Sanarwar ta ce, "Bayanan da muke da su sun nuna cewa ISIL, Al-Qaeda, Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda na shirin kaddamar da hare a yankuna da dama, musamman idan aka yi la'akari da hare-haren da aka kai kwanakin baya a a Faransa, Mali, Nigeria da Turkiyya."

Kazalika Amurka ta ja kunnen 'yan kasarta da su "sanya idanu sosai kan abubuwan da ke wakana a wuraren taruwar jama'a da kuma abubuwan hawa."

Sai dai wani jami'in hukumar tsaron kasar ya shaida wa BBC cewa ba wai kawai Amurkawa ne ke fuskantar barazana daga wajen 'yan ta'addan ba.

Miliyoyin Amurkawa ne za su fara komawa kasar a wannan makon domin yin hutun bukukuwan karshen shekara da za a yi ranar Alhamis.