'Akwai rashawa a jami'o'in Najeriya'

Hakkin mallakar hoto wiki
Image caption Daliban Nigeria sun ce suna fuskantar kalubale daga malamansu

Wasu dalibai a Najeriya sun ce matsalar cin hanci da rashawa ba wai ta tsaya ba ne kawai a kan shugabanni ba.

Daliban wadanda suke ake kammala wani taron kwanaki biyu akan matasa da cin hanci da rashawa a Najeriyar, ranar Laraban nan sun ce matsalar ta kusa har cikin jami'o'i da kwalejojin kasar.

Babban misalin da suka bayar shi ne irin yadda malaman kan tirsasa wa mata su kwana da su, kafin su yadda su ci kwasa-kwasansu.

Haka kuma sun kara da cewa wasu malaman suna tambayar dalibai kudade domin hayar da su, wanda sabanin hakan ka iya sanya malaman kayar da daliban.

Yanzu haka daliban dai suna yin kira ga gwamnati da ta fadada girman yakin da take yi da rashawa da cin hanci ya zuwa makarantun kasar.