FBI ta bankado gungun masu satar bayyanai

Hukumar bincike ta FBI ta bayana sunan mai satar bayyanai a shafukan internet da ake zarginsa da satar bayanai sama da biliyan daya adadin da ba a taba ganin irinsa.

Sunan mutumin ya bayana a cikin takardun da hukumar ta FBI ta gabatarwa kotu a bara .

Mutumin mai suna Mr Grey ana zarginsa da satar bayanai ta hanyar amfani da wani adreshin e mail daga kasar Rasha.

A baya dai Mr Grey ya dinga talata bayanan ga shafukan sada zumunta na Facebook da kuma Twitter.

Sai dai wani kamfanin tsaro na Amurka ne ya bankado satar bayyanan da kuma wani karin adreshi na e mail guda miliyan 500 a bara.

Gungun masu aikata miyagun laifuka a kasar Rasha da aka dorawa alhakin satar da aka yi wa lakabi CyberVor sun shiga cikin shafukan internet sama da 420,000, a cewar kamfanin Holdings.