An gano matukin jirgin Rasha da ya bata

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Putin ya ce Rasha za ta dauki mataki.

Kasar Rasha ta ce matukin jirginta da ya bata bayan Turkiyya ta harbo jirgin da yake ciki a kan iyakar Syria yana nan cikin koshin lafiya.

Kazalika Rasha ta ce sojin Syria ne suka tsinci matukin jirgin, kuma yana sansanin sojinta da ke Syria.

Daya daga cikin matukan jirgin da kuma wani sojan ruwa da ke cikin tawagar da ke yunkurin ceto mutanen cikin jirgin, sun mutu.

Turkiya ta ce ta harbo jirgin ne saboda ya keta sararin samaniyarta, ko da ya ke Shugaba Vladimir Putin ya musanta hakan, yana mai cewa harbo jirgin tamkar wani "yankan baya" ne daga wajen masu mara wa 'yan ta'adda baya.

Lamarin dai ya sa an fara tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Rasha da Turkiya.

A nasa bangaren, shugaban Amurka Barack Obama ya ce kasarsa tana goyon bayan matakin da Turkiyya ta dauka na harbo jirgin saman Rasha.

Shugaba Obama ya bayyana matsayin Amurka ne a lokacin da yake tattaunawa ta waya da takwaransa na Turkiyyar Recep Tayyip Erdowan, ko da ya yake sun amince da su yayyafa wa wutar rikicin ruwa.

Majalisar dinkin duniya da kungiyar tsaro ta NATO sun ja hankalin Rasha da Turkiyya da su magance matsalar da ta taso a tsakaninsu.