An kori 'yan Nigeria daga Biritaniya

Image caption Akasarin mutanen sun ce ba su da 'yan uwa a Najeriya don haka ba su san inda za su ba.

Wani jirgin sama dauke da wasu 'yan asalin Najeriya da aka kora daga Biritaniya ya sauka a filin jiragen saman Lagos.

Akasarin mutanen da aka kora sun ce ba su ji dadin hakan ba.

Daya daga cikinsu ya shaida wa wakilin BBC cewa 'yan sandan Biritaniya sun kama shi, kuma ba su bar shi ya dauki ko da tsinke ba kafin su saka shi a jirgi.

Wasu daga cikinsu sun ce ba su da dangi a Najeriya don haka ba su san inda za su je ba.

A kwanakin baya ne Najeriya ta nuna rashin jin dadinta da sanarwar da Biritaniya ta yi cewa za ta kori 'yan Najeriya 29,000 daga kasar, tana mai cewa bai kamata a kore su ba har sai an bi ka'ida.

Najeriya dai ta bukaci Biritaniya ta tabbatar cewa mutanen da za ta kora 'yan Najeriya ne kuma suna da koshin lafiyar da za su iya fita daga kasar.