Jirgin sama marasa matuki da zai rika sa ido kan bola

Hakkin mallakar hoto NCSIST

An soma gwajin wani jirgin sama marasa matuki da ke da naura ta musaman da za ta dinga sa ido a kan iskar da ke tashi daga tarin bola ko shara.

Jirgin saman marasa matuki zai yi tafiya a saman filayen 200 da ke Birtaniya domin nazari a kan gurbatacciyar iskar da ake fitarwa a kasar.

Kiyasin baya bayanan ya nuna cewa abincin da ake bukata na samar da tan miliyan 21 na gurbataciyyar iska a kowace shekara a kasar ta Birtaniya.

Jami'ar Manchester tare da hadin gwiwar hukumar kula da muhali ta Birtaniya suka dauki nauyin gwajin.

A cewar Doug Wilson wanda jami'i ne a hukumar muhalin ya ce , bincike ya biyo bayan bukatar da ake akwai wajen samar da hanya mafi sauki da za ta rika sa ido a kan matsalar.