An sace man fetur na biliyan 50 - NNPC

Image caption Kamfanin NNPC ya ce fasa bututun mai na jawo wa Nigeria asara sosoi.

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, ya ce an yi asarar lita miliyan 531 na man fetur wanda kudinsa ya kama naira biliyan 50, sakamakon barnar da barayin bututun mai suka yi tsakanin watannin Janairu da Satumbar 2015, a wasu layukan bututu da aka shimfida su daga jihar Legas zuwa birnin Ilorin.

A wani jawabi da ta gabatar a gaban kwamitin man fetur na majalisar dattawan kasar, Manajan Daraktar hukumar kula da bututun mai na kamfanin PPMC, Mrs. Esther Nnamdi-Ogbue, ta ce asarar da aka samu ta faru ne sakamakon fashe-fashen bututun man fetur a yankunan Arepo da Mosimi, wanda hakan ya sanya ake samun matsalar fitar da man.

Sai dai Mrs Nnamdi-Ogbue ta ce duk da kalubalen da ake fuskanta a layukan bututun da aka shimfida daga Lagss zuwa birnin Ilorin din, PPMC zai ci gaba da kokarin tabbatar da cewa kasar ta samu isasshen man fetur din da ake bukata wajen loda mai daga daffo din dake Lagos da Oghara da kuma na baya-bayan nan da ke Calabar.

Kazalika, Shugabar hukumar PPMC ta kara da cewa wasu dillalan mai marasa kishin kasa ne ke dakile kokarin da hukumar ke yi na kawar da layuka a gidajen mai a fadin kasar, inda suke ayyukan da basu dace ba, kamar sayar da man a kasuwannin bayan fage.

Hukumar ta tabbatar da cewa tana duba hanyoyin da za ta bi wajen tabbatar da cewa an samu mafita ta din-din-din ga wannan matsala ta rashin mai, inda ta ce akwai bukatar a gina wani rumbu na adana isasshen man fetur.