"Sulhu tsakanin Musulmai da Kiristoci na da muhimmanci"

Image caption An yi ruwa kamar da bakin-kwarya a Nairobi.

Paparoma Francis ya ce tataunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban abu ne mai matukar wuya amma tana da muhimmancin gaske.

Paparoma ya bayyana haka ne a ganawar da ya yi da Musulmai da Kiristocin kasar Kenya a ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka.

Da yake jawabi kan harin da masu ikirarin kishin Musulinci suka kai a babban kantin nan na sayar da kayayyaki da ke Nairobi, Westgate da kuma Jam'iar Garrisa, Paparoma Francis ya ce bai kamata mutane su rika yin amfani da sunan Allah domin su nuna kiyayya ga wasu mutane ba.

A bangare guda, Paparoma ya gudanar da taron addu'oi a Jam'iar Nairobi.

An tsaurara tsaro a Jami'ar, inda 'yan sanda da sojoji suka yi binciken kwakwaf kan mutanen da suka shiga wajen addu'oin.

A rika mutunta al'adun gargajiya

Dubban mutane ne suka halarci wajen yin addu'oin, inda Paparoma ya bukaci mutane da su rika mutanta al'adunsu na gargajiya

Image caption Paparoma ya bukaci 'yan kasar Kenya da su yi riko da al'adunsu na gargajiya.

Paparoman ya ce, "Zaman lafiyar kowacce al'umma ya dogara ne kan zaman lafiyar iyali".