Ruwan sama ya yi barna a Saudiya da Qatar

Ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya, a Qatar da Saudiyya ya dakatar da harkoki a kasashen biyu.

Ruwan saman da ya zuba a sa'a daya, ya kai kwatankwacin na shekara daya.

Ruwan ya toshe hanyoyi da dama kuma ya tilastawa makarantu da shaguna rufewa.

A Saudiya, ruwan yayi ambaliya a kan hanyoyi kuma motoci sun nutse a karkashin ruwan a baban birnin Saudiya, Riyadh.

Ruwa ya yi ta tsiyaya daga rufin filin jiragen sama na Hamad da ke Qatar, wanda aka bude a bara.

Firai ministan Qatar ya bayar da umarnin a gudanar da bincike a kan kyawun gine-ginen da ake yi a filin jiragen saman Qatar, a wani bangare na shirye-shiryen daukar nauyin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekarar 2022.