An kashe mutane 3 a harbe-harbe a Amurka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan sanda a Colorado

'Yan sanda a Colorado na Amurka sun ce an kashe mutane 3, a wasu harbe-harben da aka yi a wata cibiyar tsarin iyali.

Wani dan bindiga ne ya bude wuta a wurin, wanda kungiyar kayyade iyali ta Planned Parenthood ke tafiyar wa.

An dauki sa'o'i 7 ana harbe-harben kafin daga baya dan bindigan ya bada kai ga 'yan sanda.

Magajin garin birnin John Suthers ya ce wadanda aka kashe sun hada da farar hula biyu da kuma jami'in dan sanda guda.

Wasu mutane 9 da suka hada da 'yan sanda sun jikkata a lamarin.

Har yanzu dai ba a gano nufin kaddamar da harin ba.

Kungiyar kayyade iyali ta Planned Parenthood dai ta sha fuskantar bore daga wurin wadanda suke adawa da zubar da ciki.