Hollande ya sha alwashin murkushe 'yan ta'adda

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban kasar Faransa Francois Hollande

Shugaba Hollande na Faransa ya sha alwashin murkushe abin da ya kira gungun masu tsatstsaurar akida da suka kai harin bindiga da bama - bamai a Paris makwanni biyun da suka wuce.

Da yake jawabi a wajen taron tunawa da mutanan da lamarin ya ritsa da su, Mr Hollande ya ce Faransa za ta ci gaba da girmama abubuwan da mutanan da suka mutu suke girmamawa da kuma yadda rayuwa take a Faransa.

Sannan ya ce wadanda suka mutu a hare-haren, an kashe su ne a lokacin da suke wakiltar 'yancin kai.

Mr Hollande ya kuma bayyana godiyarsa ga goyan bayan da Faransa ta samu daga kasashen duniya.