An sace 'yan Poland a Nigeria

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Jirgin ruwa

Gwamnatin kasar Poland ta ce an sace wasu ma'aikatan jirgin ruwa su biyar ciki har da matukin jirgin da kuma wasu ma'aikata uku a cikin wani jirgi da ke tafiya a kan ruwan Najeriya.

Ministan harkokin wajen Poland Witold Waszczykowski ya ce an sace mutanen ne a daren ranar Alhamis daga jirgin ruwan mai suna Szafir.

Haka kuma wasu ma'aikatan jirgin 11 sun tsira bayan da suka buya a cikin jirgin.

Babu labarin cewa an samu rauni ko kuma an ga jini a cikin jirgin.

Ministan ya ce jirgin ruwan ya lalace bayan da maharan suka bude masa wuta.

Waszczykowski ya ce yanzu suna jira su ji daga wajen wadanda suka sace ma'aikatan jirgin ko kuma daga gwamnatin Najeriya domin su ga ko za a iya daidaitawa.

Jirgin dai na kan hanyarsa ne daga Belgium zuwa Najeriya inda yake dauke da wasu manyan karafa da sauran kayayyaki.