Paparoma ya yi suka kan masu kudi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Paparoma ya ce ya kamata kowanne dan adam ya samu abubuwan more rayuwa.

Paparoma Francis ya yi suka kan tsirarun masu kudi saboda nuna halin ko-in-kula kan talakawa.

Paparoma ya yi wannan suka ne a lokacin da ya kai ziyara wani yankin marasa galihu da ke wajen birnin Nairobi, a kasar Kenya.

Mutane sun yi dandazo a lokacin da Paparoma ya kai ziyara yankin Kangemi, inda masara galihu kimamin dubu 50 ke zama ba tare da samun abubuwan more rayuwa ba.

Ya ce masu kudi suna boye arzikinsu, kuma hakan yana sanya wa talakawa na rayuwa cikin kunci.

A ranar Alhamis, lokacin da Paparoma ya kai ziyara a ofishin majalisadr dinkin duniya da ke Nairobi, ya ce akwai bukatar kowanne dan adam ya samu abubuwan more rayuwa.