Rasha za ta taya Faransa yaki da IS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugabannin Russia da Faransa

Rasha ta amince da ta yi aiki tare da Faransa wajen yaki da kungiyar jihadi ta IS.

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ne ya bayyana hakan a karshen wata tattaunawa da shugaban Faransa, Francoise Hollande a Moscow.

Mista Putin ya ce kasarsa za ta hada kai da Faransa da sauran sojin kawancen Amurka ta fuskar musayar bayanan soji.

Ya kara da cewa Rasha za ta kauce wa fito-na-fito da sauran sojojin da suke yakar kungiyar ta IS.

Sai dai kuma alamu na nuna cewa Rasha ba za ta shiga kawancen soji tare da Amurka ba.