An gano kaburbura a Iraqi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kaburbura

Mahukunta a arewacin Iraqi sun gano wasu kaburbura wadan da a ke kyautata zaton gawawwakin mutane fiye da dari na wadanda 'yan kungiyar IS suka kashe ne.

Wannan shi ne karo na shida da a ke gano kaburbura a kusa ko kuma a cikin garin Sinjar tun bayan lokacin da 'yan kungiyar IS su ka kwace ikonsa.

Masu ikirarin jihadin sun kashe al'ummar Yazidi 'yan tsiraru, kana sun bautar tare da yiwa mata fyade bayan sun kwace garin a shekarar da ta gabata.

'Yan IS na daukar 'yan Yazidi a matsayin wadan da ba sa bin tafarki ma dai-daici.