Dan wanzan ya rasu

Image caption Ranar Asabar aka yi jana'izar Muhammadu Danmalam, wato Dan Wanzam

Shararren dan wasan nan na kwaikwayon barkwaci a Najeriya , Dan wanzan na Sokoto ya rasu.

Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Sama'ila Na Abba Afakallah ne ya tabbatarwa da BBC labarin rasuwar dan wasan, wanda aka yi ta yadawa a kafar sada zumunta na Intanet.

Marigayin ya rasu a ranar juma'a da dare za kuma a yi jana'izar sa a yau Asabar.

Dan wanzan ya yi suna a wasanin kwakwaikwayo na barkwanci a inda ya ke fitowa a matsayin wanzami a shirin talbijin.