An kona fina-finai a Kano

kone fina-finai
Image caption Shugaban gudanarwar hukumar tace fina finai da sauran jami'an gwammnati na duba fina finan da aka kama kafin a cinna musu wuta

Hukumar tace fina finai ta jihar Kano ta yi bikin kona fina-finan batsa a jihar.

Shugaban gudanarwar hukumar Sheikh Bazallah Nasiru Kabara shi ya jagoranci kona fina-finan a harabar ofishin hukumar da ke Kano a ranar Alhamis.

A cewar wani jami'in hukumar, yawan fina finan da aka kona sun kai sama da 1,000 kuma an kama su ne a lokuta daban daban a sumamen da hukumar ta kai a wuraren da ake sayar da fina-finai a cikin jihar.